Shugaba Tinubu Ya Yi Ƙaramin Sauyi a Majalisar Ministoci, Edun da Ɗangiwa Sun Bar Muƙamansu


Shugaban ƙasa, , ya amince da yin wani ƙaramin sauyi a cikin Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), inda wasu ministoci biyu suka bar muƙamansu tare da naɗa sababbin waɗanda za su maye gurbinsu.

Sanarwar ta fito ne daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), inda ya sanya hannu kan wata takarda da ke bayyana matakin.

A cewar sanarwar, tsohon Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziƙi, Wale Edun, ya bar muƙaminsa, kuma an umurce shi da ya miƙa ragamar aiki ga Taiwo Oyedele, wanda yanzu aka ɗaga shi zuwa matsayin Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki. Kafin wannan naɗin, Oyedele ya kasance Ƙaramin Minista a ma’aikatar.

Haka kuma, an sanar da cewa Ahmed Musa Ɗangiwa zai bar muƙaminsa na Ministan Gidaje da Raya Birane, yayin da aka gabatar da Muttaqha Rabe Darma a matsayin sabon minista a wannan ma’aikata.

Takardar ta kuma umarci dukkanin ministocin da abin ya shafa da su kammala dukkan hanyoyin miƙa mulki da karɓar aiki kafin ƙarshen aiki na ranar Alhamis, 23 ga Afrilu, 2026.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO