Sauya Shekar Obi Zuwa ADC Ya Tayar Da Hankalin Gwamnati – Yusuf Tanko
Shugaban Ƙungiyar Magoya bayan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyar Labour Party, Peter Obi, wato Yusuf Tanko, ya ce sauya sheƙar da Obi da wasu fitattun ‘yan siyasa suka yi zuwa jam’iyyar (ADC) ta firgita gwamnatin da ke kan mulki gabanin zaɓen 2027.
Tanko ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television, inda ya ce ƙaruwar goyon bayan jama’a ga jam’iyyar ADC na nuna cewa zaɓen 2027 zai kasance mai zafi da gasa mai tsauri.
Comments
Post a Comment