Sanata Yayi Ya Fito Takarar Gwamnan Ogun

Sanata Solomon Adeola, wanda aka fi sani da Yayi, ya sanar da shiga takarar gwamnan Jihar Ogun a karkashin jam’iyyar APC domin zaben shekarar 2027.

Dan majalisar mai wakiltar yankin Ogun West ya sayi fom din tsayawa takara na jam’iyyar APC kan kudi har Naira miliyan 50 a birnin Abuja a yau.

Babban Sakataren Tsare-tsare na Kasa na jam’iyyar APC, Suleiman Argungu, ne ya mikawa wakilin Sanata Yayi takardun fom din a madadinsa.

Wannan mataki na nuna cewa Sanata Yayi ya fara shirin fafatawa a hukumance domin neman kujerar gwamnan jihar Ogun gabanin babban zaben shekarar 2027.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO