Sanata Kabiru Gaya Ya Fice Daga APC Yana Shirin Komawa ADC
Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Ibrahim Gaya, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar (APC).
Rahotanni sun bayyana cewa Sanata Gaya ya rubuta takardar murabus inda ya aika ta ga shugabannin jam’iyyar a matakin ƙaramar hukuma a mazaɓarsa ta Gaya.
A cikin takardar, ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne bayan dogon tunani da tuntuɓa da magoya bayansa da al’ummar mazaɓarsa, yana mai cewa lokaci ya yi da zai ɗauki sabon matakin siyasa domin ciyar da muradun jama’a gaba.
Rahotanni sun nuna cewa Sanata Kabiru Gaya yana shirin komawa jam’iyyar ADC ne domin ci gaba da fafutukar siyasa.
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya na daga cikin fitattun ‘yan siyasa a Kano, inda:
Ya taɓa zama gwamnan Jihar Kano daga shekarar 1992 zuwa 1993.
Ya kuma yi shekaru da dama yana wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa ta ƙasa.
Comments
Post a Comment