Rahoto: Naira Tiriliyan 34.44 Daga Cikin Tiriliyan 84 Ba Su Kai Asusun Tarayya Ba —Peter Obi
Peter Obi ya ce wannan giɓi na kuɗi ya janyo damuwa kan yadda ake tafiyar da kuɗaɗen gwamnati da kuma buƙatar ƙara inganta tsarin sa ido da gaskiya wajen sarrafa kuɗaɗen shiga.
Tsohon ɗan takarar ya nuna damuwa tare da gargadin cewa matsalar na nuna akwai kalubalen a cikin tsarin tafiyar da kuɗaɗen gwamnati, yana mai nuni da cewa ƙasar na fuskantar matsin lamba daga matsalolin cikin gida da ke shafar tattalin arziki.
Masana na ganin ya zama dole hukumomin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike domin gano haƙiƙanin inda kuɗaɗen suka tafi tare da ɗaukar matakan da suka dace domin kare dukiyar ƙasa da inganta gaskiya a harkokin kuɗi.
Comments
Post a Comment