Peter Obi Ya Yi Kira Ga ‘Yan Najeriya Su Tashi Tsaye Don Kare Dimokuraɗiyya
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su haɗa kai domin kare dimokuraɗiyya tare da hana ƙasar komawa tsarin jam’iyya guda ɗaya.
A cikin wani saƙo da ya wallafa, Obi ya bayyana cewa shi da sauran shugabanni da mambobin jam’iyyar ADC tare da sauran ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa suna nuna damuwa kan makomar dimokuraɗiyyar Najeriya.
Ya ce:
“Mu, mambobi da shugabannin jam’iyyar ADC, tare da sauran ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da son dimokuraɗiyya, muna cewa bai kamata a kashe dimokuraɗiyyarmu ba.”
Obi ya jaddada cewa dole ne a guji duk wani yunƙuri na mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya guda ɗaya, yana mai cewa hakan zai iya kawo barazana ga haɗin kai, zaman lafiya da tsaron ƙasa.
Ya kuma yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya da suka yi imani da haɗin kai, zaman lafiya da tsaro su tashi tsaye domin kare dimokuraɗiyya da tabbatar da adalci a cikin tsarin siyasa.
Masu sharhi na siyasa na ganin wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun muhawara kan makomar siyasar ƙasar da kuma zargin yunƙurin ƙarfafa jam’iyya guda ɗaya a gabanin zaɓen shekarar 2027.
Comments
Post a Comment