Osifo:Gwamnati Na Da Dama Ta Taimaka wa Matatar Ɗangote Don Rage Farashin Man Fetur

Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, TUC, Festus Osifo, ya yi tir da hauhawar farashin mai a ƙasa, yana mai cewa yana kan hanyar kaiwa Naira 2000. 

A cewar Osifo, wannan hauhawar na faruwa ne saboda yaƙin da ke gudana tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran.

Osifo ya bayyana cewa, idan farashin man fetur ya tashi fiye da tsarin kasafin Kuɗin da aka shirya a cikin kasafin Kuɗin Najeriya, hakan na haifar da yawan kuɗi ga gwamnati. A wannan yanayin, ya bayyana cewa gwamnati na da dama ta amfani da rarar kuɗaɗen da ba a tanada ba wajen samar da tallafin man fetur.

Shugaban Ƙwadagon ya ba da shawara cewa gwamnati ta ɗauki aƙalla kashi 60 cikin ɗari na wannan rara da aka samu ba tare da an tsara shi ba, domin tallafa wa man da ake tura wa Matatar Man Dangote domin rage farashin man fetur a ƙasa.

#BreakingNews #FestusOsifo #FarashinMai #DangoteRafinery

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO