Mutumin Da Ya Mayar Da Naira Miliyan 2.2 Da Aka Tura Masa Bisa Kuskure Ya Bayyana Dalilin Ƙin Karɓar Kyautar N50,000
Wani mutum ya bayyana dalilin da ya sa ya ƙi karɓar kyautar Naira dubu 50 da aka ba shi bayan ya mayar da Naira miliyan 2.2 da aka tura masa cikin asusun OPay ɗinsa bisa kuskure.
Rahotanni sun nuna cewa kudin sun shiga asusun mutumin ne, mai suna Tunde Muhammad Elyaƙub, ba tare da saninsa ba, amma yana fahimtar cewa Kuɗin ba nasa ba ne, ya gaggauta tuntuɓar mai kuɗin domin mayar masa da su gaba ɗaya ba tare da rage ko sisin kwabo ba.
Bayan an dawo da kuɗin cikin nasara, wanda ya yi kuskuren tura kuɗin ya nuna godiyarsa ta hanyar ba mutumin kyautar Naira dubu 50 a matsayin lada kan gaskiya da amincinsa. Sai dai ElYaqub ya ƙi karɓar kudin, yana mai cewa bai yi abin don a biyashi ba, illa kawai ya yi abin da ya dace a matsayin nagartaccen ɗan ƙasa.
Ya ƙara da cewa karɓar irin wannan kyauta zai iya rage darajar gaskiya da amana da ya yi ƙoƙarin nunawa, yana mai jaddada cewa yin abin kirki bai kamata ya zama saboda neman wani sakamako ba.
Lamarin ya jawo yabon jama'a da dama a shafukan sada zumunta, inda mutane ke yabawa mutumin bisa nuna gaskiya, riƙon amana da kyawawan halaye a cikin al'umma.
Comments
Post a Comment