Mummunan Hari a Kasuwar Jilli Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Da Dama a Jihar Yobe
A ranar Asabar, dab da Magriba, wani mummunan hari da jirgin yaƙi ya kai a kasuwar Jilli ya jawo asarar rayukan fararen hula masu yawan gaske a ƙaramar hukumar Geidam, jihar Yobe, bayan da aka yi tsammanin cewa ‘yan ta’adda ne ke taruwa a wannan kasuwa.
Yadda lamarin ya faru
Rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin yaƙi ne ya zuba wuta kan jama’a da suka taru suna gudanar da kasuwar kauye a garin Jilli da ke yankin Fuchimiram. An ce harin ya auku ne a lokacin da mutane ke saye da sayarwa, lamarin da ya jefa al’umma cikin tashin hankali da firgici mai tsanani.
Wata majiya ta bayyana cewa tun da farko gwamnatin jihar Yobe ta rufe kasuwar saboda barazanar ‘yan ta’addan Boko Haram da ake zargin suna amfani da wurin wajen harkokinsu, lamarin da ya sa ake zargin taron jama’ar ya saɓa da umarnin tsaro.
Asarar rayuka da halin da ake ciki
Rahotanni na farko sun nuna cewa an samu asarar rayuka da dama sosai, inda ake hasashen kusan mutane fiye da ɗari biyu suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata.
A halin yanzu, an kwashe waɗanda suka jikkata zuwa babban asibitin gwamnati da ke Geidam, inda ake ci gaba da ba su kulawa ta gaggawa.
Kansila mai wakiltar Jilli, Hon Lawal Zannah Nur, ya bayyana cewa ana matuƙar buƙatar gudummawar jini daga al’umma domin ceton rayukan waɗanda suka jikkata a asibiti.
Comments
Post a Comment