🔥Malami Ya Sha Alwashin Ceto Kebbi, Ya Ce Babu Ja Da Baya
Tsohon Ministan Shari’a na Tarayya, Abubakar Malami, ya bayyana cewa kudirinsa na ceto da farfaÉ—o da jihar Kebbi ba zai taÉ“a sauyawa ba. Tsohon Ministan ya faÉ—i hakan ne a yayin da tarin magoya baya suka tarbe shi a filin jirgin sama suka kuma rakashi zuwa ofishin jam'iyyar ADC na jihar Kebbi.
Abubakar Malami ya jaddada cewa babu ja da baya ko miÆ™a wuya a wannan tafiya, yana mai nuna Æ™warin gwiwa cewa jihar Kebbi za ta samu ci gaba ta hanyar haÉ—in kai da taimakon Allah, tare da kira ga al’umma su mara masa baya domin cimma burin sauyi da ci gaba.
Comments
Post a Comment