Magoya Bayan Peter Obi Sun Yi Kira Da A Yi Zanga-Zangar Ƙasa Domin Mamaye Ofishin INEC
Magoya bayan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyar Labour Party a zaɓen shekarar 2023, Peter Obi, sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su fito zanga-zanga a faɗin ƙasar nan domin mamaye ofisoshin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, wato (INEC), domin kare dimokuraɗiyya.
Kungiyar ta bayyana cewa manufar zanga-zangar mai taken #OccupyINEC ita ce nuna rashin amincewa da wasu matakai da suke ganin na iya jefa Najeriya cikin tsarin jam’iyya ɗaya kacal, abin da suka ce zai zama barazana ga dimokuraɗiyya da ‘yancin zaɓen jama’a.
A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar, ta jaddada cewa Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya wadda dole ne a kiyaye tsarin jam’iyyu da dama, tare da tabbatar da cewa kowace jam’iyya na da damar yin takara cikin adalci da gaskiya.
Sun ce duk wani yunƙuri da zai taƙaita gasa tsakanin jam’iyyu ko kuma ya bai wa jam’iyya ɗaya rinjaye na dindindin zai iya jawo rikici da rashin zaman lafiya.
Kungiyar ta kuma bukaci magoya bayanta da sauran ‘yan ƙasa su fito cikin lumana domin nuna damuwarsu, tare da kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi yayin gudanar da zanga-zangar.
Comments
Post a Comment