Kotu Ta Haramta wa INEC Amincewa da Babban Taron da Kwamitin Rikon Ƙwarya na ADC Ya Shirya
Kotun Tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Justice Joyce Abdulmalik, ta bayar da umarni da ya hana Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) amincewa ko halartar duk wani taron na jihohi da kwamitin rikon ƙwarya na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ke shiryawa.
A hukuncin da kotun ta yanke, ta kuma hana tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark, da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar katsalandan cikin ayyuka da wa’adin shugabannin jihohi na jam’iyyar da aka zaɓa bisa ƙa’ida.
Wannan hukunci ya biyo bayan ƙarar da Norman Obinna tare da wasu mutum shida suka shigar a madadin shugabannin jam’iyyar na jihohi, inda suka ƙalubalanci sahihancin kwamitin riƙon ƙwarya na ƙasa, suna zargin cewa ba shi da ikon doka ko kundin tsarin jam’iyya na shirya babban taron na jihohi ko naɗa kwamitocin gudanar da su.
Kotun ta kuma soke naɗin wani kwamitin shirya babban taron da ake kira “congress committee”, tana mai cewa tsarin da aka bi ba ya cikin kundin tsarin jam’iyyar, sannan ta umarci cewa shugabannin jihohi da aka zaɓa su ne kaɗai ke da ikon shirya duk wani taro.
Comments
Post a Comment