Jihohin Arewa 5 Za su Kasance Cikin Duhu Daga Afrilu 9 Zuwa Mayu 2 Inji Kamfanin Wutar Lantarki
Hukumar Hukumar Samar da Wutar Lantarki mai zaman kanta ta Najeriya (NISO) a taƙaice, ta sanar da al’ummarta a jihohin Adamawa, Gombe, Bauchi, Borno da Yobe cewa su shirya wa katsewar wutar lantarki a layin wutar Jos–Gombe 330kV daga ranar Alhamis 9 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu, 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa katsewar wutar za ta riƙa faruwa ne domin ba da damar gudanar da gyaran manyan kayayyakin lantarki da sabunta tsarin sadarwa na wutar lantarki, wanda ake sa ran zai inganta samar da wuta a yankin bayan kammala aikin.
Jihohin da abin zai shafa: Adamawa, Gombe, Bauchi, Borno da Yobe
Lokacin katsewar: Daga 9:00 na safe zuwa 6:00 na yamma
Kwanakin katsewar: Daga Alhamis zuwa Lahadi a duk mako
Dalili: Gyara da sabunta layin wutar lantarki na Jos–Gombe 330kV
Hukumar NISO ta buƙaci al’umma da su yi haƙuri tare da ɗaukar matakan kariya, tana mai jaddada cewa aikin zai taimaka wajen inganta ɗorewa wutar lantarki da rage yawan matsalolin ɗaukewar wuta a nan gaba.
Comments
Post a Comment