Jama'atu Nasril Islam Ta Ce An Kashe Musulmi 4, Wasu 10 Sun Ɓace A Harin jihar Filato

Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta bayyana cewa aƙalla Musulmi huɗu ne aka kashe, yayin da wasu goma kuma suka ɓace sakamakon mummunan hari da aka kai ranar Lahadi a jihar Filato. 

A cikin wata sanarwa da Ƙungiyar ta fitar, ta nuna matuƙar damuwa kan yadda hare-haren ke ci gaba da faruwa a yankin, tare da kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kungiyar ta ce bayan tattara bayanai daga majiyoyinta a yankin, an tabbatar da mutuwar mutane hudu daga cikin Musulmi, yayin da har yanzu ake neman wasu mutum goma da ba a san inda suke ba tun bayan harin.

Rahotanni sun nuna cewa wannan hari na daga cikin jerin hare-haren da suka janyo asarar rayuka da dama a Jihar Plateau, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin al’umma a fadin kasar.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO