INEC Ta Cire Sunayen Shugabannin ADC Daga Rajista Saboda Rikicin Cikin Gida
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, ta (INEC), ta cire sunayen shugabannin Kwamitin Gudanarwa na jam’iyyar (ADC) daga rajistarta sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar.
Rahotanni sun nuna cewa matakin ya biyo bayan umarnin kotu, inda INEC ta bayyana cewa ba za ta amince da kowanne ɓangare na jam’iyyar ba har sai an warware taƙaddamar shugabanci da ke tsakanin ɓangarorin da ke rikici.
An ce sunayen shugabannin ɓangaren da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ke jagoranta ne aka cire daga rajistar hukumar.
Masu lura da al’amuran siyasa sun yi gargaɗi cewa wannan rikici na iya kawo cikas ga shirin haɗakar jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027, musamman idan jam’iyyar ta kasa gabatar da ɗan takara da INEC za ta amince da shi.
A gefe guda kuma, jam’iyyar ADC ta zargi jam’iyyar (APC) da hannu wajen haddasa matsalolin da ke faruwa a cikin jam’iyyar.
Comments
Post a Comment