Hukumar NDLEA ta Kama Mai Shekaru 93 Da likita Mai Shekaru 69 Da Laifin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
Hukumar NDLEA ta gudanar da gagarumar samame a wasu jihohin Najeriya, inda ta kama wasu mutane masu ban mamaki ciki har da wani tsoho mai shekaru 93 da kuma wani likita mai shekaru 69 bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
A cewar hukumar, an gudanar da kamen ne ne ta hanyar sahihan bayanan sirri da kuma aikin leƙen asiri da aka shirya tsaf domin fatattakar masu harkar miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar.
A cewar Hukumar NDLEA, an kama tsohon mai shekaru 93 a wani samame da jami’anta suka kai bayan samun sahihan bayanan sirri.
A wani aikin daban kuma, an kama likita mai shekaru 69 da ake zargi da hannu wajen safarar hodar ibilis da kuma wiwi.
An gudanar da dukkanin samamen ne a wurare daban-daban a jihohi daban-daban na ƙasar.
Comments
Post a Comment