Harbin ’Yan Bindiga Ya Jikkata Sheikh Maharazu Mafara a Zamfara



Wani fitaccen malamin addini kuma tsohon shugaban ƙaramar hukuma, Sheikh Abdullahi Maharazu Mafara, ya tsallake rijiya da baya bayan da wasu ’yan bindiga suka buɗe masa wuta a kan hanya a jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da Sheikh Maharazu ke kan hanyarsa daga Talata Mafara zuwa Gusau domin halartar wani muhimmin taron jam’iyyar (APC), inda maharan suka kai masa hari tare da harɓe motarsa.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa malamin ya samu raunuka a ƙafarsa sakamakon harbin, inda likitoci suka yi nasarar cire harsashin da ya same shi. A halin yanzu, ana kula da lafiyarsa a asibitin koyarwa na jami'ar Usmanu Danfodiyo, da ke Sokoto, (UDUTH), kuma rahotanni sun nuna cewa yana samun sauƙi.

Lamarin ya sake tayar da hankulan al’umma dangane da matsalar tsaro a yankin, musamman a wasu sassan jihar Zamfara, inda hare-haren ’yan bindiga ke ci gaba da barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ana sa ran hukumomin tsaro za su fitar da ƙarin bayani kan lamarin nan gaba kaɗan.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO