Gwamnatin Yobe Ta Amince da Ɗaukar Ɗalibai 416 Da Suka Kammala Kwalejin Jinya ta Damaturu


Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da ɗaukar ma’aikata kai tsaye daga ɗalibai 416 da suka kammala karatu a Kwalejin Kimiyyar Jinya ta Shehu Sule da ke Damaturu.

Sabbin ma’aikatan da za a ɗauka sun haɗa da Community Nurses su158, da Basic Nurses da kuma Ungozomomi guda 196, tare da dalibai 62 da suka kammala matakin Babbar Difloma ta Higher National Diploma (HND) a fannin jinya daga kwalejin.

Gwamna Buni ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye ɗaliban jinya da ungozoma da aka gudanar a birnin Damaturu, inda ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na ƙarfafa ɓangaren lafiya ta hanyar samar da ƙwararrun ma’aikata a asibitocin jihar.

A jawabinsa wanda Mataimakin Gwamnan jihar, Idi Barde Gubana, ya gabatar a madadinsa, gwamnan ya ce zuba jari da gwamnatin jihar ta yi a kwalejin na nufin magance ƙarancin ma’aikatan lafiya a cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin jihar.

Ya ƙara da cewa wannan mataki na daga cikin sauye-sauyen da gwamnatin jihar ta ƙaddamar a ɓangaren lafiya, wanda tuni ya fara haifar da sakamako mai kyau wajen inganta ayyukan kiwon lafiya da kula da lafiyar al’umma.

Gwamnatin jihar ta kuma buƙaci sabbin ma’aikatan da aka ɗauka su kasance masu kishin aiki, biyayya ga dokokin sana’a, tare da ba da gudunmawa wajen bunƙasa harkokin kiwon lafiya a Jihar Yobe.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO