Gwamnatin Tinubu Ta Amince da Biyan Naira Tiriliyan 3.3 Domin Gyara Matsalar Wutar Lantarki
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da shirin biyan bashin da ya kai naira tiriliyan 3.3 domin warware tsofaffin basussukan da suka daɗe suna addabar ɓangaren wutar lantarki a Najeriya tun daga shekarar 2015 zuwa Maris 2025.
Sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce an riga an fara aiwatar da shirin, inda tashoshin samar da wutar lantarki 15 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar karɓar kuɗaɗe da suka kai naira tiriliyan 2.3.
Gwamnatin Tarayya ta tanadi naira biliyan 501 domin fara biyan bashin, inda aka riga aka fitar da naira biliyan 223, yayin da ake ci gaba da sauran biyan kuɗaɗen.
A cewar mai ba shugaban ƙasa shawara kan makamashi, Olu Arowolo-Verheijen, shirin zai taimaka wajen tabbatar da daidaito a samar da wutar lantarki, jawo sabbin jari, samar da ayyukan yi, da inganta ayyukan kasuwanci da masana’antu.
Shugaba Tinubu ya kuma tabbatar da cewa mataki na gaba na shirin gyaran ɓangaren wutar lantarki (Series II) zai fara a wannan zangon shekara.
Comments
Post a Comment