GAGGAWA: Olusegun Obasanjo, Atiku Abubakar, da Rabiu Musa Kwankwaso Sun Hallara a Ibadan Domin Taron Dabarun Siyasa
Wasu manyan jagororin adawa a Najeriya, ciki har da tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, sun hallara a birnin Ibadan domin gudanar da wani muhimmin taron sirri kan makomar siyasar ƙasar.
Rahotanni sun ce taron ya mayar da hankali ne kan yadda jam’iyyun adawa za su haɗa kai domin tinkarar babban zaɓen shekarar 2027, tare da duba hanyoyin magance matsalolin tattalin arziƙi da tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Majiyoyi sun bayyana cewa taron ya samu halartar wasu fitattun ‘yan siyasa da tsofaffin gwamnoni daga sassa daban-daban na ƙasar, inda aka tattauna yiwuwar kafa haɗaka tsakanin jam’iyyun adawa domin ƙarfafa tasirinsu a zaɓe mai zuwa.
Ana sa ran irin wannan ganawa za ta ci gaba a nan gaba yayin da ake ƙara tunkarar zaɓen 2027, wanda masana siyasa ke ganin zai kasance ɗaya daga cikin zaɓukan da za su fi ɗaukar hankali a tarihin siyasar Najeriya.
Comments
Post a Comment