🎗️Fiye da Yara Falasɗinawa 350 ne Ke Tsare a Gidajen Yarin Isra'ila — Kungiyoyin Kare Hakkoki Sun Yi Gargadi

Fiye da yara Falasɗinawa 350 ne har yanzu ke tsare a gidajen yari a daidai lokacin da ake bikin Ranar Yara ta Duniya, lamarin da ya jawo damuwa daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin Falasɗinawa sun bayyana cewa yaran na fuskantar tsananin take haƙƙi, ciki har da kama su da ƙarfin tuwo, killace su na tsawon lokaci a keɓe, da kuma tsare su ba tare da gurfanar da su a kotu ba.

Rahotanni sun nuna cewa irin waɗannan matakai na faruwa ne akai-akai, inda ƙungiyoyin suka zargi hukumomi da aiwatar da tsare-tsare na zalunci ga yara a yankunan Falasɗinu.

Ƙungiyoyin sun yi kira ga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da su gaggauta ɗaukar mataki domin kare rayuka da martabar waɗannan yara, tare da neman a sako su ko a bi hanyoyin shari’a da suka dace.

Lamarin na zuwa ne a lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan halin da yara ke ciki a yankunan da ake fama da rikici, musamman a yankin Gabas ta Tsakiya.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO