🔴Dubban Matasa Sun Ziyarci Gidan Jonathan a Abuja, Sun Nemi Ya Koma Siyasa
ABUJA – Dubban matasa da Ƙungiyoyin farar hula sun mamaye hedkwatar tsohon shugaban Æ™asa, Goodluck Ebele Jonathan, a Abuja ranar Laraba, suna kira da ya tsaya takarar shugaban Æ™asa a zaÉ“en 2027, amma dai Jonathan bai bayyana ba.
Masu zanga-zangar sun fito daga jihohi daban-daban na Najeriya, suna rera waƙoƙi da rawar gargajiya, ɗauke da tambura masu nuna goyon bayansu kamar:
“GEJ: Najeriya na cikin haÉ—ari, ka yi ceto!”
“GEJ, idan ba ka tsaya ba, mu kuma ba za mu daina ba.”
Shugaban Æ™ungiyar “Coalition for Goodluck Jonathan”, Dr. Tom Ohikere, ya shaida wa manema labarai cewa sun gudanar da tattaunawa da bincike a faÉ—in Æ™asar na tsawon watanni shida kafin su kira Jonathan. Ya bayyana tsohon shugaban a matsayin mutumin da zai iya haÉ—a kan Najeriya da kawo sauyi mai É—orewa.
Comments
Post a Comment