Dalilin Ficewar Marafa Daga Jam’iyyar ADC Zuwa NDC Ya Bayyana

Rahotanni sun tabbatar da cewa Sanata Kabiru Marafa bai samu tabbacin samun tikitin takarar gwamnan jihar Zamfara a jam’iyyar (ADC) ba, lamarin da ya tilasta masa ficewa daga jam’iyyar tare da komawa sabuwar jam’iyyar National Democratic Congress (NDC), makonni kaɗan bayan da ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa ADC saboda rashin jituwa ta cikin gida.

Marafa, wanda ke da burin tsayawa takarar gwamnan jihar Zamfara a zaɓe mai zuwa, an ruwaito cewa ya samu tabbacin tikitin takarar gwamna a sabuwar jam’iyyar ta NDC, lamarin da ya ja hankalin masu lura da lamuran siyasa a jihar.

Sauyin sheƙar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin manyan ‘yan siyasa na ci gaba da sake tsara matsayinsu gabanin zabukan da ke tafe.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO