DALIBAN JIHAR NIGER DA SUKA MAKALE A JOS SUN KOKA, SUN NEMI A KWASO SU CIKIN GAUGAWA SAKAMAKON HARE-HAREN ‘YAN TA’ADDA
Wasu dalibai ‘yan asalin Jihar Niger da ke karatu a jami’o’i daban-daban a Jos, babban birnin Jihar Plateau, sun koka kan halin da suke ciki bayan sun maƙale a garin sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda da suka yi sanadin asarar rayuka da jikkata mutane da dama.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne a yankin Angwan Rukuba a ranar Lahadi, inda aka kashe sama da mutane 20 tare da jikkata wasu da dama. Lamarin ya haifar da fargaba a faɗin garin Jos, lamarin da ya sa ɗalibai da dama suka kasa fita daga gidajensu ko kuma suka tsere daga dakunan kwanan ɗalibai domin tsira da rayukansu.
Ɗaliban na Jihar Niger sun bayyana cewa har yanzu ba a kai musu ɗauki ba, duk da cewa wasu jihohi sun riga sun kwashe ɗalibansu daga Jos domin kare lafiyarsu. Sun ce suna rayuwa cikin tsoro, wasu kuma sun fara fuskantar ƙarancin abinci da kuɗin kashewa.
A cikin koken da suka yi, ɗaliban sun yi kira ga gwamnatin Jihar Niger da ta gaggauta ɗaukar matakin kwashe su daga Jos cikin gaggawa, domin kauce wa faɗawa cikin haɗari idan hare-haren suka sake tsananta.
A bangare guda, hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa suna ƙara yawan sintiri da ɗaukar matakan tsaro a yankunan da abin ya shafa, yayin da gwamnatin tarayya ta ba mazauna Jos tabbacin cewa za ta yi duk mai yiwuwa domin dawo da zaman lafiya a yankin.
Comments
Post a Comment