Da Ɗumi-ɗumi: Sanata Nakudu da Wasu Fitattun 'Yan Siyasar Jigawa Daga PDP, APC Sun Koma ADC
Jigawa – Fitattun ‘yan siyasa daga APC, NNPP da PDP sun yi babban sauyin sheƙa zuwa (ADC) a jihar Jigawa.
Sanata Sabo Muhammad Nakudu ya jagoranci wannan sauyi, inda ya bayyana cewa ya bar APC don shiga jam’iyya wadda za ta mayar da hankali kan ci gaban talakawa da adalci a siyasa. Nakudu ya kuma sanar da niyyarsa ta tsayawa takarar gwamna a zaɓen 2027 karkashin tutar ADC.
Baya ga Nakudu, wasu fitattun ‘yan siyasa sun shiga ADC, ciki har da:
Bala Ibrahim Chamo, tsohon shugaban Karamar Hukumar Dutse
Zakari Kafin Hausa, tsohon mashawarci na musamman ga gwamna Umar Namadi
Wasu tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi daga Gwaram da Ringim
Masu sharhi na siyasa sun ce wannan yunkuri na ADC zai iya sauya tasirin jam’iyyun siyasa a jihar kafin babban zaben 2027.
Comments
Post a Comment