🚨 Da Ɗumi-ɗumi: Ana Zargin An Tilasta Shugaban INEC Fitar da Sanarwa Kan ADC Saboda Barazanar Murabus


Fitaccen lauya kuma masani kan harkokin kare haƙƙin É—an Adam, Chidi Odinkalu, ya yi zargin cewa an matsa wa shugaban hukumar zaÉ“e Mai zaman kanta (INEC), Joash Amupitan, lamba domin ya fitar da wata sanarwa da ta shafi cire ko dakatar da hulÉ—a da É“angarorin jam’iyyar (ADC).

Odinkalu ya ce an yi masa barazanar amfani da wata takardar murabus da aka riga aka sanya wa hannu, idan har bai bi umarnin wasu masu iko ba.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin shugabanci da ke cikin ADC ya kai ga matakin da INEC ta dakatar da hulÉ—a da dukkan bangarorin jam’iyyar, tare da cire wasu sunaye daga tsarin ta har sai kotu ta yanke hukunci na Æ™arshe. 

Masu ruwa da tsaki a ADC sun yi zargin cewa akwai yunÆ™urin matsa wa hukumar zaÉ“e lamba domin raunana jam’iyyar gabanin zaÉ“en 2027, musamman bayan Æ™aruwar shigowar manyan ‘yan siyasa cikin jam’iyyar.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO