BREAKING: Wani Bayahude Ya Roƙi Shugaban Amurka Ya Rushe Isra’ila, Ya Ce Ita Ce Barazana Ga Duniya
Wani Bayahude mai tsattsauran ra’ayi ya jawo cece-kuce bayan ya buƙaci Shugaban Amurka, Donald Trump, da ya rusa ƙasar Israel gaba ɗaya, yana mai cewa ƙasar ba ta wakiltar Yahudawa na gaskiya ba kuma ita ce babbar barazana ga Yahudawa da duniya.
Rahotanni sun ce mutumin ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai hedikwatar InfoWars a birnin Austin a ranar 29 ga Afrilu.
Ana danganta wannan ra’ayi da wasu daga cikin al’ummar Yahudawa masu adawa da kafuwar ƙasar Isra’ila, lamarin da ya haifar da muhawara a kafafen sada zumunta.
Comments
Post a Comment