Birtaniya Ta Ce Tana Sanya Ido Kan Zaɓen Najeriya na 2027

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewa tana sanya ido sosai kan shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027 a Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa matakin na Birtaniya na nufin bibiyar yadda ake shirya zaɓen domin tabbatar da an gudanar da shi cikin gaskiya da adalci, ba tare da katsalandan cikin harkokin cikin gida na Najeriya ba.

A nata ɓangaren, hukumar Shirya  Zaɓe Ta Ƙasa Mai zaman kanta (INEC) ta ce tana ci gaba da shirye-shiryen da suka haɗa da inganta rajistar masu kaɗa ƙuri’a da kuma haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

Ana sa ran zaɓen shekarar 2027 zai kasance muhimmin mataki ga dimokuraɗiyyar Najeriya, yayin da ƙasashen duniya ke ci gaba da bibiyar shirye-shiryen zaɓen.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO