Atiku Ya Ziyarci Kwankwaso A Gidansa
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ziyarci jagoran siyasa, kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar NNPP, a shekarar 2023, Dr Rabiu Musa Kwankwaso, inda suka tattauna kan makomar jam’iyyar ADC da hanyoyin tabbatar da kyakkyawan shugabanci ga al’umma.
Atiku ya bayyana cewa sun yi tattaunawa mai amfani kan yadda za su ci gaba da aiki domin farfaɗo da jam’iyyar da kuma samar da sauyi mai ma’ana ga jama’a.
Ganawar na zuwa ne a lokacin da manyan ‘yan siyasa ke ci gaba da haɗa ƙarfi a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, lamarin da ke ƙara ɗaukar hankalin masu bibiyar siyasar Najeriya.
Comments
Post a Comment