An Zargi Trump Da Raina Addinin Musulunci Bayan Kalaman Da Ya Wallafa
Kungiyar kare hakkin Musulmi ta Amurka, Council on American-Islamic Relations, ta fito fili ta yi Allah-wadai da kalaman, Shugaban Amurka Donald Trump, da ya yi da suka shafi addinin Musulunci, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a fadin duniya, cewa irin waɗannan kalamai na iya haifar da rashin fahimta da kuma tayar da husuma tsakanin al’umma.
Trump dai ya wallafa wani saƙo ne bayan wani samame da sojojin Amurka suka kai, inda ya bayyana nasarar a matsayin wata “mu’ujizar Easter”, sannan ya yi gargaɗi ga ƙasar Iran kan wani rikici da ya shafi tsaro.
A ƙarshen sakon nasa, Trump ya yi amfani da kalmar “Dukkan yabo sun tabbata ga Allah”, abin da wasu ƙungiyoyin Musulmi suka ce bai dace ba a haɗa lafazin addini da saƙon barazana ko rikici.
Comments
Post a Comment