An Kashe Ɗan Bautar Ƙasa A Rikicin Jos Ranar Kammala Hidimarsa ta Ƙasa
Wani mummunan al’amari ya faru a birnin Jos, inda aka kashe wani ɗan bautar ƙasa (NYSC) mai suna Haruna Ibrahim a yayin rikicin da yayi sanadiyar asarar rayuka da dama, a daidai ranar da yake shirin kammala hidimarsa ta ƙasa.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayin yana cikin masu bautar Ƙasa da suka halarci bikin Kammalawa hidimar ƙasa, lokacin da rikici ya ɓarke a wasu sassan birnin inda ya rasa ransa sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan hare-haren da suka faru a wasu al’ummomi a jihar.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun fara bincike domin gano musabbabin rikicin tare da kamo waɗanda ke da hannu a cikin lamarin.
Iyalan marigayin da abokan aikinsa sun bayyana kaɗuwarsu kan rasuwar tasa, musamman ganin cewa hakan ya faru ne a ranar da ya kamata ya yi murna da kammala bautar ƙasa.
Ana ci gaba da samun tashin hankali a wasu sassan jihar Filato, yayin da hukumomi ke ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da tabbatar da tsaro a yankunan da abin ya shafa.
Comments
Post a Comment