🔴Ɗan Ganduje, Abdulaziz, Ya Fice Daga APC, Ya Koma ADC Bayan Ganawa Da Kwankwaso
KANO – ÆŠan fari ga tsohon gwamnan Jihar Kano kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na Æ™asa, Abdulaziz Umar Ganduje, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC, inda ya koma jam’iyyar ADC bayan ganawa da jagoran siyasa a jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Rahotanni sun bayyana cewa Abdulaziz ya karÉ“i katin zama memba na jam’iyyar ADC a mazabarsa ta Ganduje da ke Æ™aramar hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano, lamarin da ya tabbatar da sauya sheÆ™arsa a hukumance.
Bayan shiga jam’iyyar, an ce ya kai ziyara ga Kwankwaso domin nuna biyayya da kuma tattauna makomar siyasar sa a sabuwar jam’iyyar.
Ana iya tunawa cewa Abdulaziz Umar Ganduje ya taÉ“a tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai a zaÉ“en shekarar 2023 a mazabar Dawakin-Tofa/Tofa/Rimin Gado, amma bai samu nasara ba bayan ya sha kaye a hannun É—an takarar jam’iyyar NNPP.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin wannan sauya sheÆ™a na iya haifar da sabon salo a siyasar Kano, musamman ganin kusancin dangantakar siyasa tsakanin iyalan Ganduje da manyan jam’iyyun siyasa a jihar.
Comments
Post a Comment