ƳAN BINDIGA SUN KASHE BASARAKE, MATARSA, ƊANSA DA WASU BIYU A JIHAR BENUE


Akalla mutane biyar, ciki har da wani basarake, da matarsa, da ɗansa da kuma wasu mutum biyu, sun mutu sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a ƙauyen Olegabulu da ke ƙaramar hukumar Agatu a jihar Benue.

Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne ba zato ba tsammani, inda suka kashe waɗanda abin ya shafa tare da haddasa tashin hankali da fargaba a tsakanin mazauna yankin.

Zuwa lokacin kammala wannan rahoto, jami’an tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan musabbabin harin ba, sai dai ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO