ADC Ta Zargi INEC da Hana Ta Shiga Zaɓen 2027, Ta Bukaci A Janye Matakin Gaggawa

Jam’iyyar (ADC) ta zargi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, (INEC), da ɗaukar matakin da ka iya hana jam’iyyar shiga zaɓen shekarar 2027, inda ta buƙaci a gaggauta janye wannan mataki domin kauce wa rikici da dokar zaɓe.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta bayyana cewa INEC ta daina karɓar wasiƙu da sauran muhimman takardu daga gare ta, bisa hujjar cewa akwai shari’ar rikicin shugabanci da ke gaban kotu.

Sai dai ADC ta ce wannan mataki na iya jefa jam’iyyar cikin matsala, domin dokar zaɓe ta tanadi cewa dole ne jam’iyyun siyasa su ba da sanarwar aƙalla kwanaki 21 kafin gudanar da manyan ayyuka kamar tarurruka ko zaɓen fidda gwani.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa idan aka ci gaba da ƙin karɓar wasiƙunta, hakan na iya sa ta kasa cika sharuɗɗan doka, wanda daga baya za a iya amfani da shi a matsayin dalilin hana ta tsayar da ’yan takara a zaɓen 2027.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga sauyin shugabanci da aka samu a jam’iyyar tun a shekarar 2025, lokacin da wani sabon shugabanci ya bayyana, lamarin da wasu ’yan jam’iyyar suka kai ƙara a kotu.

Kotun dai ta bayar da umarnin a ci gaba da bin halin da ake ciki har sai an yanke hukunci a kan shari’ar.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO