🔥 ZARGIN TAYAR DA ƘURA: Tinubu Na Shirin Mayar da Hedikwatar Najeriya Zuwa Legas a 2027 — Timi Frank
🔥 ZARGIN TAYAR DA ƘURA: Tinubu Na Shirin Mayar da Hedikwatar Najeriya Zuwa Legas a 2027 — Timi Frank
Tsohon Mataimakin Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar (APC), Timi Frank, ya yi zargin cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na da niyyar mayar da babban birnin Æ™asar nan daga Abuja zuwa Lagos idan ya sake lashe zaÉ“en shekarar 2027.
Frank ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya zargi gwamnatin Tinubu da abin da ya kira manufar fifita Legas a kan sauran sassan ƙasar.
A cewarsa, matakan da gwamnatin shugaba Tinubu ke É—auka suna nuna wata manufa ta ware wasu yankuna daga cin gajiyar ayyukan gwamnati. Ya ce mafi yawan manyan shawarwari da tsare-tsaren gwamnatin suna karkata ne domin amfanin jihar Legas.
“Yanzu ya zama a fili cewa shirin shugaban Æ™asa na dogon lokaci shi ne tara iko na siyasa da tattalin arziki a Legas idan aka sake ba shi dama a karo na biyu,” in ji Frank.
Tsohon jigon na APC ya kuma yi zargin cewa naɗe-naɗen mukaman gwamnati da ayyukan raya ƙasa a ƙarƙashin shugaba Tinubu sun fi karkata ga ɓangare guda, yana mai gargadin cewa irin wannan yanayi na iya kawo barazana ga haɗin kan ƙasa.
Frank ya tambayi inda yarjejeniyoyin fahimta (MOUs) na gwamnati suke dangane da bunÆ™asa noma da kiwo a Arewa, ci gaban masana’antu a Kudu maso Gabas, da kuma haÉ“aka harkokin mai da gas a Kudu maso Kudu.
Ya ƙara da cewa:
“Babu wani shugaban Æ™asa a tarihin Najeriya da ya raba al’umma bisa yankuna da Æ™abilanci kamar yadda ake gani a wannan gwamnati.”
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa kai tsaye daga fadar shugaban ƙasa ko gwamnatin tarayya da ta tabbatar ko musanta wannan zargi.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa batun sauya babban birnin ƙasa abu ne mai matuƙar wahala, domin yana buƙatar amincewar majalisar dokoki ta ƙasa da kuma manyan sauye-sauyen kundin tsarin mulki.
Comments
Post a Comment