‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sa-Kai Uku Tare da Kwace Bindigoginsu A Zamfara
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari a ƙauyen Magamin Diddi da ke ƙaramar hukumar Maradun a Jihar Zamfara, inda suka kashe mutum uku na 'yan sa Kai wato Community Protection Group (CPG) bayan musayar wuta mai tsanani.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen ne da yawansu, inda suka fafata da jami’an tsaron al’ummar da ke kokarin kare yankin. An ce an yi musayar harbe-harbe tsakanin ɓangarorin biyu kafin daga bisani ‘yan bindigar su rinjayi jami’an CPG.
Mutanen uku da suka rasa rayukansu an bayyana sunayensu da Nasiru Gaji, Jamilu Ibrahim da Bashar Dan Inna. Bayan harin, maharan sun tsere daga yankin tare da kwace bindigogin da jami’an tsaron al’ummar ke amfani da su.
Majiyoyi sun ce daga baya an kwashe gawarwakin wadanda aka kashe zuwa Babban Asibitin Maradun, inda aka gudanar da binciken likitoci kafin daga bisani aka mika su ga iyalansu domin yi musu jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci.
Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun ƙara tsaurara matakan sintiri a duk fadin ƙaramar hukumar Maradun domin farautar maharan da suka tsere tare da dakile sake aukuwar irin wannan hari. Haka kuma an bukaci mazauna yankin su kasance cikin shiri tare da kai rahoton duk wani motsi na mutane masu tayar da hankali ga hukumomi.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga, inda ake kai farmaki kan al’umma, sace mutane da kuma kwace makamai daga jami’an tsaro ko kungiyoyin sa-kai.
Comments
Post a Comment