Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 a Wani Mummunan Hari a Jihar Flato
Rahotanni daga Jihar Flato sun tabbatar da cewa akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai wani mummunan hari a ƙauyen Wanka da ke gundumar Keram a ƙaramar hukumar Kanam.
An ce harin ya faru ne da yammacin ranar Juma’a, inda maharan suka shiga cikin al’ummar ƙauyen Wanka da ke gundumar Keram, suka fara harbe-harbe tare da jefa jama’a cikin firgici.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun zo ne dauke da muggan makamai, inda suka rika kai hari kan mazauna ƙauyen ba tare da wani gargaɗi ba. A sakamakon harin, mutane akalla 10 ne suka mutu nan take, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya haddasa fargaba da tashin hankali a yankin, inda wasu daga cikin mazauna garin suka tsere zuwa ƙauyuka da ke makwabtaka domin neman mafaka.
Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa harin ya zo musu ba zato ba tsammani, suna masu kira ga hukumomin tsaro da su ƙara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankin.
Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, jami’an tsaro ba su fitar da cikakken bayani a hukumance kan harin ba, amma ana sa ran hukumomi za su fara bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan aika-aika.
Jihar Flato dai na daga cikin yankunan da ke fuskantar matsalolin tsaro a wasu lokuta, inda hare-haren ‘yan bindiga ko rikice-rikicen kabilanci kan haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
Al’umma da dama sun bukaci gwamnati da hukumomin tsaro su dauki matakan gaggawa domin dakile irin wadannan hare-hare a yankin.
Comments
Post a Comment