Yaƙin Iran Na Cin Miliyoyin Dalolin Amurka Cikin Hanzari— Hasashen Kuɗin Na Iya Kaiwa Dala Biliyan 95

A A Tijjani 
Rahotanni daga cibiyar bincike ta Center for Strategic and International Studies (CSIS) sun nuna cewa kuɗin da kasar Amurka ta ke kashewa wajen hare-haren soja kan Iran na ƙaruwa cikin gaggawa, lamarin da ke haifar da muhawara kan tsadar wannan rikici idan ya ci gaba.

Bisa ƙididdigar da CSIS ta fitar, an kiyasta cewa Amurka ta kashe kusan dala biliyan 3.7 cikin awanni 100 na farko na hare-haren. Rahoton ya kuma nuna cewa jimillar kuɗin da aka riga aka kashe sun wuce dala biliyan 5, kuma ana ci gaba da kashe ƙarin kuɗi cikin sauri.

Masana tattalin arziƙi da na tsare-tsaren yaƙi na gargadi cewa idan rikicin ya kai tsawon watanni biyu, to kuɗin da za a kashe na iya kaiwa tsakanin dala biliyan 40 zuwa dala biliyan 95. Wannan hasashen ya fito ne daga masani kan kasafin kuɗi a makarantar kasuwanci ta Wharton School of the University of Pennsylvania, wato Kent Smetters.

Baya ga kuɗaɗen da ake kashewa, rahoton ya nuna cewa ana amfani da makamai masu linzami na zamani da kuma makaman kariya na sama (air defense interceptors) da yawa, abin da ke sa adadin ajiyar wadannan makamai ke raguwa cikin hanzari.

Masu sharhi kan harkokin tsaro na cewa irin wannan tsadar na iya ƙara matsin lamba ga kasafin kuɗin gwamnatin Amurka, musamman idan rikicin ya daɗe ko ya faɗaɗa zuwa wasu ƙasashe a yankin Gabas ta Tsakiya.

A lokaci guda kuma, wasu masana suna ganin cewa idan ba a samu hanyar sasanci ba, yaƙin na iya zama ɗaya daga cikin rikice-rikicen da suka fi tsada ga Amurka a cikin shekaru na baya-bayan nan.

Masu lura da al’amuran siyasa da tsaro na duniya na ci gaba da bibiyar yadda wannan rikici ke gudana, domin ganin ko za a samu sassaucin rikici ko kuma yaƙin zai ƙara tsananta a kwanaki masu zuwa.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO