Yadda Fasinjoji da Dama Suka Jikkata Sakamakon Hatsarin Jirgin Ƙasa A Hanyar Abuja
Fasinjoji da dama sun jikkata bayan wani hatsari da ya afku da jirgin ƙasa a layin Abuja–Kaduna a safiyar Litinin, kusa da tashar jirgin ƙasa ta Asham.
Kamfanin Nigerian Railway Corporation (NRC) ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 10:30 na safe yayin da jirgin ke kan tafiya a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Yadda hatsarin ya faru
Babban Daraktan NRC, Kayode Opeifa, ya ce rahotannin farko sun nuna cewa injin na baya ya bugi kujerun fasinjoji da ke gabansa sakamakon wata matsala ta haɗin injinan jirgin.
A cewarsa, wannan matsalar ta jawo tangarda ga jirgin, lamarin da ya sa wasu fasinjoji suka samu raunuka daban-daban. Sai dai ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ba a hatsarin.
An kai waɗanda suka jikkata asibiti
Jami’an gaggawa sun isa wurin da hatsarin ya faru nan take, inda aka ba waɗanda suka jikkata kulawar farko kafin a kai su asibitoci da ke kusa domin samun kulawar likitoci.
Bayan cire injin da ya jawo matsalar da kuma wasu kawunan jirgi da abin ya shafa, jirgin ya ci gaba da tafiya zuwa tashar jirgin ƙasa ta Idu a Abuja, inda ya isa da jinkirin mintuna 38 daga lokacin da aka tsara.
An fara bincike kan hatsarin
Hukumar Binciken Hadurra Ta Kasa wato NSIB ta ce ta tura jami’anta wurin domin gudanar da cikakken bincike kan abin da ya jawo hatsarin, tare da gano hanyoyin da za a hana faruwar makamancin haka nan gaba.
Kamfanin Sufurin jiragen kasa na Najeriya wato NRC ya jaddada cewa tsaron fasinjoji shi ne babban abin da suka fi mayar da hankali a kai, yana mai cewa za su ɗauki duk matakan da suka dace domin tabbatar da cewa zirga-zirgar jiragen ƙasa ta ci gaba cikin aminci.
Tarihin matsalolin jiragen ƙasa
A shekarun baya-bayan nan, layin jirgin Abuja–Kaduna ya fuskanci matsaloli da dama, ciki har da hatsurran jirage da kuma binciken da majalisar dattawa ta Najeriya ta ƙaddamar domin gano dalilan da ke haddasa yawaitar irin waɗannan matsaloli a sashen jiragen ƙasa.
Comments
Post a Comment