Wata Mai Rajin Neman Zaman Lafiya A Arewa Ta Nemi A Ɗauki Mataki Kan George Udom
RANAR JUMA’A, 20 GA MARIS, 2026
Fitacciyar mai fafutukar zaman lafiya tsakanin addinai a Najeriya, Magret Esabella Tanko, ta fito karara ta yi kakkausar suka ga wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ta bayyana a matsayin “karya mai hatsari” da ka iya haddasa rikicin addini.
Wani mai amfani da kafafen sada zumunta mai suna George Udom ne ya yi zargin cewa ana farautar Kiristoci a Arewacin Najeriya kamar dabbobi, inda ya ce ana kai hare-hare kan ƙauyukan Kiristoci, ana harbin jama’a yayin bukukuwan Sallah, har ma da zargin yin hadayar jini da mutane a lokacin Idi.
Sai dai a cikin wani bidiyo da ta fitar, Tanko ta musanta waɗannan zarge-zarge baki ɗaya, tana mai cewa wannan bayani ƙarya ce tsagwaronta wadda za ta iya tayar da zaune tsaye tsakanin Musulmi da Kiristoci.
Ta ce: “Ko kai Kirista ne, ka san wannan magana ƙarya ce marar tushe. Ya ce ana kai hari ranar Sallah, alhali kuwa Sallah ba ta faru ba a lokacin da yake wannan zance. Ta yaya zai ce tun jiya ana yin hakan, alhali Sallah yau ce?”
Tanko ta kuma yi tambaya kan rashin hujjoji a cikin zargin, tana cewa:
“Wane ƙauye aka kai hari? Ina aka yi hakan? Idan za ka yi zargi, ya kamata ka kawo hujja. Wannan ba magana ba ce mai ma’ana.”
Ta jaddada cewa irin waɗannan kalamai na iya haddasa mummunar illa ga zaman lafiya, tana mai gargadi da cewa:
“Irin wannan rubutu na iya rusa zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kiristoci. Ba mu yarda da wannan ba. Idan za ka faɗi ra’ayinka, ka yi da gaskiya, ba da ƙarya ba.”
A ƙarshe, Tanko ta yi kira ga hukumomi da su dauki mataki kan irin wannan lamari, tare da kira ga al’umma da su guji yaɗa bayanan da ka iya tunzura rikici.
Ta ƙara da cewa: “Muna son zaman lafiya a Arewa. Ba ma son duk wani abu da zai haddasa rikici. Duk wanda ya san wannan mutumin ya kamata ya ja masa kunne.”
Wannan martani na Tanko ya zo ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da bukukuwan ƙaramar Sallah (Eid al-Fitr), wanda aka tabbatar zai gudana a ranar Juma’a, 20 ga Maris, 2026, bayan rashin ganin jinjirin wata a ranar da ta gabata.
Masu lura da al’amura sun bayyana cewa, a irin wannan lokaci mai muhimmanci, ya zama wajibi ga jama’a su tabbatar da sahihancin bayanai kafin yaɗawa, domin kaucewa haddasa tashin hankali a tsakanin al’umma.
Comments
Post a Comment