Wani Dan Najeriya Ya Bukaci Mexico Ta Yi Watsi Da Jakadancin Reno Omokri

Wani ɗan Najeriya mai suna Valentine Obienyem ya rubuta wasiƙa ga shugabar ƙasar Mexico, Claudia Sheinbaum inda ya bayyana damuwa kan nadin Reno Omokri a matsayin jakadan Najeriya a ƙasar Mexico.

A cikin wasiƙar da ya aikawa fadar shugaban ƙasar, Obienyem ya nuna cewa nadin Omokri na iya haifar da matsala ga dangantakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Mexico.

 A cewarsa, tarihin halayen Omokri a bainar jama’a da kuma yadda yake sauya matsayi kan batutuwan siyasa na iya sanya shakku kan dacewarsa da wakiltar Najeriya a ƙasashen waje.

Obienyem ya ce kafin da kuma lokacin zaɓen shugaban ƙasa na Najeriya na shekarar 2023, Omokri ya kasance ɗaya daga cikin masu sukar shugaba Bola Ahmed Tinubu sosai.

Ya ce Omokri ya halarci zanga-zanga tare da yin maganganu masu tsauri a kafafen sada zumunta inda ya tambayi cancantar Tinubu na shugabanci tare da yin zarge-zarge kan lafiyarsa da halayensa.

A wasiƙar, Obienyem ya kuma ce nadin Omokri ya jawo muhawara a cikin Najeriya, inda wasu ‘yan ƙasa da kungiyoyin fararen hula suka nuna rashin amincewarsu da dacewarsa da mukamin jakada.

Ya ƙara da cewa akwai yiwuwar irin halayen Omokri na neman kusanci da masu iko su iya janyo matsalar watsa bayanai marasa inganci ga gwamnatin ƙasar da zai wakilta a cikinta.

Saboda haka, ya buƙaci gwamnatin Mexico da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar da su yi taka-tsantsan wajen karɓar takardun shaidar jakadancin Omokri.

Obienyem ya jaddada cewa ya rubuta wasiƙar ne saboda kishin ƙasa da kuma damuwa kan mutuncin dangantakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Mexico.

Idan ana buƙata, ya ce a shirye yake ya gabatar da ƙarin hujjoji ko bayanai da suka shafi kalaman Omokri a bainar jama’a.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO