Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Yi Muhimmiyar Ganawa da Maiɗakin Sarkin Fulanin Zamfara
Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Her Excellency Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta gudanar da wata muhimmiyar ganawa da Uwargidar Sarkin Fulanin Zamfara, kuma tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Maru da Bunguɗu, wato iyalinsa, Hajiya Habiba Shehu Danfulani.
Ganawar ta gudana ne cikin yanayi na mutunta juna da fahimtar juna, inda bangarorin biyu suka tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi cigaban Jihar Zamfara, musamman a fannin inganta walwalar mata da ƙananan yara a faɗin jihar.
Majiyoyi sun bayyana wa jaridar Zancen Yau 247 cewa, tattaunawar ta mayar da hankali ne kan hanyoyin da za a ƙara ƙarfafa shirye-shiryen tallafawa mata, bunƙasa ilimin yara, da kuma samar da ingantattun tsare-tsare da za su taimaka wajen rage matsalolin da mata da yara ke fuskanta a al’umma.
Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da haɗa hannu da masu ruwa da tsaki, musamman shugabannin al’umma da iyalansu, domin tabbatar da cewa an samar da yanayi mai kyau da zai inganta rayuwar mata da ƙananan yara a Zamfara.
A nata ɓangaren, Hajiya Habiba Shehu Danfulani ta yaba da ƙoƙarin Uwargidan Gwamnan wajen jajircewa wajen kawo sauyi mai ma’ana a rayuwar mata da yara, tare da nuna shirinta na bada gudunmawa domin cimma burin cigaban al’umma.
Ganawar dai na daga cikin matakan da ake ɗauka na ƙarfafa haɗin kai tsakanin shugabanni da al’umma domin samar da ci gaba mai ɗorewa a Jihar Zamfara.
Comments
Post a Comment