Trump Zai Kawar da Wasu Shugabannin Afirka Nan Gaba– Primate Ayodele

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya yi gargadin cewa shugaban Amurka Donald Trump na da niyyar ganin an cire wasu shugabannin ƙasashen Afirka daga kan mulki.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Oluwatosin Osho, ya fitar, malamin ya ce akwai alamun cewa siyasar Amurka za ta taka rawa wajen sauya wasu gwamnatoci a nahiyar Afirka nan gaba kaɗan. 

Primate Ayodele ya yi iƙirarin cewa Amurka ba za ta taimaka wa wasu gwamnatocin Afirka kamar yadda ake zato ba, sai dai a cewarsa, akwai wasu tsare-tsare da za su iya janyo matsin lamba ga shugabannin da ke kan mulki.

Ya kuma yi gargadi musamman ga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa ya kamata gwamnatin ƙasar ta yi taka-tsantsan wajen hulɗar siyasa da ƙasashen waje. A cewarsa, duk da ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen magance matsalar tsaro, akwai yiwuwar Amurka ta ɗauki wasu matakai da za su iya shafar siyasar cikin gida ta Najeriya. 

Malamin ya kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ƙara himma wajen magance matsalar tsaro, yana mai gargadin cewa akwai yiwuwar samun hare-hare da kuma rikice-rikicen siyasa idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba.

Sai dai wasu masana harkokin siyasa na ganin irin waɗannan maganganu na nuna ya san gaibu ne, wadanda ba su da tabbacin faruwa a zahiri, domin dangantakar ƙasashen duniya tana tafiya ne bisa manufofi da yarjejeniyoyi tsakanin gwamnatoci.

A halin yanzu dai babu wata sanarwa daga gwamnatin Amurka ko fadar shugaban Najeriya da ta mayar da martani kan wannan ikirari na malamin cocin.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO