Tambuwal Ya Fice Daga PDP, Ya Koma Jam’iyyar ADC
Sanata Aminu Waziri Tambuwal, tsohon gwamnan Jihar Sokoto kuma mai wakiltar mazabar Sokoto ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar (PDP) tare da komawa jam’iyyar (ADC).
Tambuwal ya bayyana hakan ne a wata wasiƙa da ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na gundumarsa a Tambuwal/Shinfiri Ward da ke ƙaramar hukumar Tambuwal a Jihar Sokoto, mai ɗauke da kwanan wata 11 ga Maris, 2026. A cikin wasiƙar ya ce ficewar tasa daga jam’iyyar ta fara aiki nan take.
Tsohon kakakin Majalisar Wakilai ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne bayan yin zurfin tunani tare da shawarwari da abokan siyasa da magoya bayansa. Ya ce rikice-rikicen cikin gida da sabanin ra’ayi tsakanin shugabannin jam’iyyar sun sa ya zama da wahala ya ci gaba da zama a cikinta.
A cewarsa, rikice-rikicen da suka dabaibaye PDP sun raunana haɗin kai da kuma alkiblar da jam’iyyar ta yi fice da ita a baya.
Tambuwal ya kuma gode wa PDP bisa damar da ta ba shi wajen yi wa Najeriya hidima a fannoni daban-daban, ciki har da lokacin da ya kasance Kakakin Majalisar Wakilai da kuma gwamnan Jihar Sokoto na wa’adi biyu.
Bayan ficewar tasa, sanatan ya sanar da shiga jam’iyyar ADC tare da wasu daga cikin abokansa na siyasa da magoya bayansa. Ya ce ya yanke wannan shawara ne saboda ya yi imanin cewa Najeriya na bukatar wani dandalin siyasa mai ƙarfi da za ta ginu kan gaskiya, rikon amana, haɗin kai da kuma himma wajen ci gaban ƙasa.
Tambuwal ya jaddada kudirinsa na ci gaba da yi wa ƙasa hidima tare da kare muradun dimokuraɗiyya, adalci da haɗin kan Najeriya.
Masu sa ido kan siyasa na ganin cewa sauyin jam’iyyar na Tambuwal na iya ƙara ƙarfafa ADC yayin da ake tunkarar zaɓukan shekarar 2027.
Comments
Post a Comment