Rikicin Gabas Ta Tsakiya: Trumph Ya Ce Dangantakar Amurka da Birtaniya Ta Fara Tsami


Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa dangantakar kasarsa da Birtaniya “ba kamar yadda ta saba ba,” yana danganta sauyin ga yadda Firayim Ministan Birtaniya Keir Starmer ya jinkirta ba Amurka izinin amfani da sansanonin sojin Birtaniya wajen kai farmaki kan Iran.

A cewar Trump, wannan mataki daga Starmer ya nuna raguwar kusanci a “dangantakar musamman” da ke tsakanin kasashen biyu, musamman a lokacin da Amurka ke gudanar da hare-hare tare da Isra’ila kan Iran.

Gwamnatin Starmer ta fara da ƙin amincewa da amfani da sansanonin sojin Birtaniya domin hare-haren Amurka kan Iran, tana mai cewa an yi hakan ne don biyayya ga dokar ƙasa da ƙasa da kuma kauce wa janyo Birtaniya cikin yaki kai tsaye.

Sai dai bayan harin ramuwar gayya da Iran ta kai a yankuna daban-daban na gabas ta tsakiya—wanda ya haɗa da harin da ya shafi sansanin sojin Birtaniya na RAF a Akrotiri—Starmer ya sake duba matsayinsa, inda ya ba da izinin Amurka ta yi hare-haren kariya daga sansanonin Birtaniya kan wuraren harba makaman Iran.

Trump ya bayyana cewa jinkirin Birtaniya ya bambanta da irin goyon bayan da kasashe irin Faransa suka bayar, yana mai cewa bai dace ƙawayen tarihi su yi wata-wata a lokutan rikici ba. Ya kara da cewa Amurka “ba lallai ta dogara da Birtaniya ba” a fannin karfin soja, amma “ya kamata gwamnatin Starmer ta nuna ƙarin goyon baya.”

Martanin Birtaniya
Jami’an gwamnati a Landan sun kare matsayinsu, suna cewa duk wasu matakai ana yinsu ne bisa bukatun kasa, ba wai kin taimakon abokan hulɗa ba. Sun ce ba za su shiga wani yaki kai tsaye da Iran ba tare da hujjar doka da cikakken nazari ba.

-Lamarin ya nuna cakwakiyar sabuwar alaka tsakanin gwamnatin Trump da sabuwar gwamnatin Birtaniya.
– Yana kuma haskaka sabani tsakanin dabarun soja na Amurka da Birtaniya wajen mu’amala da Iran.
– Masu sharhi sun ce duk da jinkirin farko, Birtaniya har yanzu na nan a matsayin kawar Amurka, sai dai a cikin iyaka da kundin dokokinta.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO