NIMET Ta Gargadi Zamfara, Kano Da Wasu Jihohin Arewa Kan Hadarin Barkewar Sankarau

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da gargaɗin lafiyar jama’a inda ta ce wasu jihohin arewacin ƙasar na cikin babban haɗarin kamuwa da cutar sankarau yayin da yanayin rani mai zafi da ƙura ke ƙaruwa a sassan Najeriya. 

A cikin sanarwar da hukumar ta wallafa, ta bayyana cewa cutar sankarau wata mummunar cuta ce da ke shafar murfin da ke rufe kwakwalwa da jijiyar baya, wadda yawanci ƙwayar cuta mai suna Neisseria meningitidis ke haifarwa. Cutar na yaduwa ta hanyar ƙananan ɗigon numfashi daga mutum zuwa mutum, musamman a wuraren da cunkoso ko rashin isasshen iska yake. 

Jihohin da ke cikin haɗari
Hukumar NiMet ta bayyana jihohi 11 da ta ce suna cikin babban haɗarin kamuwa da cutar sakamakon yanayin zafi, ƙarancin danshi da kuma ƙura mai yawa. Jihohin sun haɗa da: Sokoto, da Zamfara da Kebbi da kuma Katsina. 

Sauran Jihohin su ne Kano da Jigawa da Adamawa da Gombe da Bauchi da Yobe da kuma Jihar Barno.

Hukumar ta ce waɗannan yanayi na muhalli suna samar da damar da cutar ke yaduwa cikin sauri. 

Alamomin cutar
Hukumar NiMet ta kuma bayyana cewa cutar sankarau na iya zama mai haɗari cikin sauri idan ba a gano ta da wuri ba. Daga cikin alamomin cutar akwai: zazzabi mai tsanani da ciwon kai mai ƙarfi ko taurin wuya, da amai ko tashin zuciya, sannan kuma da jin zafi idan haske ya bugi ido

Hukumar ta jaddada cewa gano cutar da wuri da kuma fara magani da gaggawa na iya rage haɗarin mutuwa da kuma matsalolin da ke biyo baya. 

Mutanen da suka fi fuskantar haɗarin Kamuwa
Hukumar NiMet ta ce mafi yawan waɗanda ke cikin haɗarin kamuwa da cutar sun haɗa da: yara da matasa da kuma mutanen da ke rayuwa a wuraren da ke da cunkoso, waɗanda ke rayuwa a wuraren da ƙura da iska mai zafi suke yawa da Kuma masu raunin garkuwar jiki


Matakan kariya
Hukumar ta shawarci jama’a su ɗauki matakan kariya domin rage haɗarin kamuwa da cutar, ciki har da: yin rigakafin cutar sankarau, da tsaftace hannu akai-akai, da gujewa cunkoso ko wuraren da iska ba ta shiga sosai, sannan kuma da zuwa asibiti da wuri idan an ga alamun cutar

A baya-bayan nan ma, Najeriya ta karɓi fiye da allurai miliyan ɗaya na rigakafin cutar sankarau, inda aka fi mayar da hankali ga mutane masu shekaru daga shekara 1 zuwa 29, domin su ne suka fi kamuwa da cutar. 

Masana lafiya sun bayyana cewa yawan bullar cutar sankarau a Najeriya na faruwa ne a lokacin rani, musamman a yankunan da ake kira “meningitis belt” na Afirka, inda zafi da ƙura ke taimakawa wajen yaɗuwar cutar. 

Hukumar NiMet ta bukaci jama’a su kasance cikin shiri tare da bin shawarwarin masana lafiya domin kare kansu da al’ummarsu daga wannan barazana ta cutar sankarau. 

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO