Malaman Addinin Kirista Sun Mamaye Ofishin Trump Don Yi Masa Addu'a.
Fastoci da jagororin addini sun roƙi Allah ya ba shugaban Amurka hikima, shiriya da kariya yayin da yake jagorantar ƙasar
Wasu fastoci da manyan shugabannin addinin Kiristoci sun hallara a ofishin Oval Office da ke cikin White House domin yin addu’a ga shugaban Donald Trump.
Rahotanni sun bayyana cewa jagororin addinin sun yi addu’o’i na musamman suna roƙon Allah ya ba shugaban Amurka shiriya, hikima da kuma kariya yayin da yake jagorantar ƙasar.
A yayin taron addu’ar, fastocin sun kuma roƙi Allah ya ba Trump ƙarfi da basira wajen yanke muhimman shawarwari da suka shafi makomar Amurka da kuma al’ummar ƙasar.
Taron addu’ar ya gudana ne a cikin ofishin shugaban ƙasar, inda ake karɓar manyan baƙi da kuma gudanar da muhimman tattaunawa kan harkokin mulki.
Masu lura da al’amuran siyasa sun ce irin wannan taro na addu’a yana nuna yadda shugabannin addini a Amurka ke taka rawa a tafiyar da mulkin kasar ta Amurka
Comments
Post a Comment