Majalisar Masarautar Zazzau ta Fitar da Tsarin Hawan Sallah na Bana

Majalisar Masarautar Zazzau ta sanar da sabon tsarin gudanar da Hawan Sallah Karama na shekarar 1447AH/2026, tare da bayyana wasu sauye-sauye da za a aiwatar a bana domin sauƙaƙa zirga-zirga da kuma tabbatar da tsaro.

A cikin wata sanarwa daga Ofishin Sakataren Majalisar, an umarci dukkan Hakimai 31 na masarautar da su bi sabuwar hanyar gudanar da hawan Sallah, musamman ma canjin hanyar shiga da fita daga fadar mai martaba.

Sanarwar ta bayyana cewa a bana an sauya tsohuwar ƙofar shiga fadar Sarkin Zazzau zuwa wata sabuwar ƙofa a Kofar Doka, wanda hakan ya sa aka sake tsara yadda jerin gwanon Hawan Sallah zai gudana.

Hawan Sallah
Majalisar ta ce da Sarkin Zazzau ya ba da umarnin dukkan Hakimai da ‘yan majalisarsu za su sauka daga doki a makarantar Alhudahuda kafin su shiga fadar mai martaba.

Daga nan kuma za a tsara jerin gwanon hawa ta hanyar bin hanya daga Lemu, zuwa Rimin Tsibiri, sannan Babban Dodo, kafin a isa filin fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau wato Malam Musa Square.

Haka kuma an sanar da cewa bas-bas da za su ɗauko Hakimai za su tsaya ne a Masallacin Mallam Musa dake hanyar Jos, daga inda mahalarta za su nufi wurin da aka tanada domin shiga jerin gwanon hawan Sallah.

Hawan Bariki
Game da Hawan Bariki, sanarwar ta ce Sarkin Zazzau tare da ‘yan majalisar masarautar za su fara taruwa ne a Filin Sukuwa na Muhammad Aminu Square a GRA, inda za a fara tafiya da misalin karfe 8:00 na safe.

Daga nan kuma Hakiman Mahaya za su isa filin da misalin karfe 9:00 na safe, kafin daga bisani a je Gidan gwamnatin Jihar Kaduna da misalin karfe 10:00 na safe domin gaisuwar Sallah ga gwamnati.

Bayan kammala wannan ziyara, Sarkin Zazzau da tawagarsa za su dawo fadar Mai Martaba domin karɓar gaisuwar jama’a da kuma ci gaba da sauran al’adun hawan Sallah.

Majalisar ta jaddada cewa ya zama wajibi ga dukkan Hakimai su zo tare da dokokinsu da kuma ‘yan canjinsu, domin su shiga cikin jerin gwanon hawan Sallah yadda ya kamata.

Haka kuma an gargadi duk wani ɗan hakimi da ya zo ba tare da doki ba, cewa hakan na iya sa a ɗauki matakin hukunci a kansa bisa dokokin masarautar.

Majalisar ta ce wannan tsari na daga cikin matakan da ake ɗauka domin tabbatar da cewa Hawan Sallah na bana ya gudana cikin tsari, martaba da kuma bin al’adun Masarautar Zazzau.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO