Kwankwasiyya Ta Yi Gargadi Kan Tsige Gwarzo
Magoya bayan Dr Rabiu Musa Kwankwaso, wato Kwankwasiyya, sun yi gargaɗi ga Majalisar Dokokin Jihar Kano da ta yi taka-tsantsan kan yunkurin tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, tana mai cewa matakin na iya haddasa sabon rikicin siyasa a jihar.
A wata sanarwa da kakakin Kwankwasiyya, Dakta Habibu Mohammad, ya fitar, ya bayyana cewa matakin tsige mataimakin gwamnan zai iya ƙara tsananta rabuwar kai a siyasance tare da barazana ga amanar da al’ummar Kano danka wa gwamnati a zaben 2023.
Ƙungiyar ta jaddada cewa nasarar da gwamnatin jihar ta samu a zaɓe ta kasance sakamakon haɗin kan dubban magoya bayan Kwankwasiyya a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar, don haka bai kamata a ɗauki matakin da zai iya karya wannan haɗin kai ba.
Zargin da Majalisar Ke Yi
Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan majalisar dokokin jihar sun sanya hannu kan takardar fara shirin tsige mataimakin gwamnan, inda suke zarginsa da saba da amana da kuma wasu batutuwan da suka shafi amfani da kuɗin gwamnati a lokacin da yake kwamishinan kananan hukumomi.
An kuma ba shi wa’adin makonni biyu domin ya kare kansa kan zarge-zargen kafin a ci gaba da matakin tsige shi idan aka gamsu da hujjojin majalisar.
Kwankwasiyya: Kada a Yi Amfani da Tsige Wa Don Siyasa
A cewar ƙungiyar Kwankwasiyya, duk da cewa kundin tsarin mulki ya ba majalisa damar sa ido kan ayyukan gwamnati, tsige wani babban jami’i mataki ne mai matuƙar nauyi wanda bai kamata a yi amfani da shi domin sasanta rikicin siyasa ko sake tsara alakar siyasa ba.
Sun ƙara da cewa duk wani mataki da zai yi kama da zalunci ko nuna wariya ga manyan jiga-jigan gwamnati zai iya tayar da hankalin magoya bayan jam’iyya da kuma al’ummar jihar baki ɗaya.
Halin Siyasar Kano
A halin yanzu dai Abba Kabir Yusuf ne ke jagorantar gwamnatin jihar tare da mataimakinsa Gwarzo, bayan sun samu nasara a zaɓen gwamna na 2023 ƙarƙashin jam’iyyar NNPP.
Masu lura da harkokin siyasa na ganin cewa wannan rikici na iya ƙara ɗumamar siyasar Kano, musamman idan aka yi la’akari da irin tasirin da ƙungiyar Kwankwasiyya ke da shi a jihar.
A ƙarshe, ƙungiyar ta buƙaci ‘yan majalisar dokokin Kano da su yi aiki cikin hikima da adalci domin kauce wa duk wani mataki da zai iya tayar da hankali ko haifar da sabuwar rikicin siyasa a jihar.
Comments
Post a Comment