Kowa Tashi Ta Fissheshi, inji Amurka Ga 'Yan Kasarta da ke Zaune A Gabas Ta Tsakiya

Ofishin Jakadun Amurka da ke Birnin Kudus da na kasar Qatar sun fitar da sanarwa a ranar Talata, inda suka bayyana cewa ba su da ikon taimaka wa ‘yan ƙasar Amurka su bar yankin Gabas ta Tsakiya a wannan lokaci.

A cewar sanarwar, rikicin da ya ɓarke tsakanin ƙasashen yankin da kuma harin ramuwar gayya da ake ci gaba da yi ya jawo matsanancin hargitsi, wanda ya sa ba a iya ba da tabbacin tsaro ko jigilar gaggawa.

Jakadancin Amurka ya ja hankalin dukkan ‘yan ƙasar da ke yankin da su kasance cikin shiri, su bi ka’idojin tsaro na cikin gida, sannan su guji barin gidajensu ba tare da buƙatar gaggawa ba. Haka kuma, an shawarce su da su ci gaba da bibiyar shafukan yanar gizon jakadancin don sabbin umarni ko sanarwa.

Sanarwar ta kuma ce, saboda rashin tsaro da tsananin rikici, hukumomin Amurka ba za su iya ba da tallafin tashi da jirgin ƙasa ko na ruwa ba, kuma yakamata ‘yan ƙasar su yi nazari kan yuwuwar zaɓin barin yankin ta hanyar jiragen kasuwanci idan har ana samun su.

Wannan umarni ya ƙara ƙara fargabar da ke kara yaɗuwa a tsakanin ‘yan ƙasar waje da ke rayuwa ko yawon buɗe ido a yankin, musamman ganin yadda rikicin ya lafa amma ba ya nuna alamar sauka.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO